Wasu ‘yan bindiga sun kai hari bankuna biyu a garin Anyigba da ke karamar hukumar Dekina a jihar Kogi, inda suka kashe ɗan sanda daya da wani mutum guda.

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafofin sa da zumumta ya nuna cewa ‘yan bindigar sun kai mummunan hari kan bankunan da misalin karfe 5 na yammacin Alhamis.


Ganau sun ce maharan sun buɗe wuta a bankunan wadanda sun shahara da kuma caji ofis din garin, kana suka yi awon gaba da makudan kuɗin da ba a tantance adadinsu ba.
Yan fashin da suka shiga garin sun fara kai farmaki ofishin ‘yan sanda da ke kan titin Anyigba-Idah, inda suka kashe dan sandan da aka bayyana sunansa da Idoko.
Majiyar ta ce ɗan sandan da aka kashe bai jima da komawa aiki a ofishin ba kuma ya fito ne daga Iyale, wani gari da ke makwabtaka da karamar hukumar.
Bayan haka kuma ƴan fashi da makamin sun kashe wani mutumi mai suna, Alagama, wanda yana talla a bakin titi, ba zato harsashin maharan ya yi ajalinsa.
Ganau ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun biyo motar ɗauko kuɗin bankin zuwa ofishinsu da ke Anyigba, inda suka ci ƙarfin jami’an tsaro kafin su kwashe duka kudaden.
Bugu da ƙari, wata tawaga da ake zaton tana cikin ƙungiyar ƴan fashin ta kutsa kai cikin wani fitaccen banki da ke garin, nan ma suka yi awon gaba da kuɗi masu yawa.
Jami’an ƴan sanda a jihar ba su ce komai dangane da lamarin ba zuwa yanzu.
