A yau musulmi a Najeriya da wasu ƙasashen duniya su ka fara azumtar watan Ramadan.

Wannan dai shi ne azumin da za a yi na shekarar 2024.
An fara azumin watan ne bayan da aka samu umarni daga sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar lll da ya bayar da tabbacin ganin jinjirin watan a jiya Lahadi.

A wasu jihohin na Najeriya an yi zafi da rana wanda hakan ya sa da dama mutane su ka ɗauke ƙafa a waau titunan na wasu johohin ƙasar.

Ana sa ran za a yi azumi 29 ko 30 kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
