Mabiya mazahabar Shi’a a Najeriya sun yi zanga-zangar lumana tare da huƙatar a tsagaita wuta a hare-haren da aka tsananta kaiwa zirin gaza.

An yi zanga-zangar a jihohin Kano, Sokoto, Legas, Zamfara, Katsina, Bauchi, Gombe, Kaduna Adamawa, Yobe da babban birnin tarayya Abuja.

A Abuja, an masu zamga-zangar sun ƙone tutocin kasar Amuruka da Burtaniya a ofishin jakadancin Amuruka.

Masu zanga-zangar sun buƙaci shugaban ƙasar Amuruka Joe Biden da ya janye dukkanin goyon bayan da yaje yi wa Isra’ila domin daƙile kisan gilla da ake yi wa mata da ƙananan yara a Gaza.

A wata sanarwa da Sheik Sidi Munis Mainasara Sokoto mamba a ƙungiyar ya fitar, sun buƙaci a gaggauta tsagaita wuta a hare-haren da ake kaiwa.

Duk da kasancewar ana cikin watan Ramadan, hakan bai hana ci gaba da kai hare-hare a Gaza ba wanda Isra’ila ke yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: