Babbar kotun jihar Ekiti ta yankewa wani da ta samu da aikata fashi da makami hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yankewa Bello Abdulquadiri hukuncin ne bayan kamashi da aka yi a ranar 8 ga watan Maris ɗin shekarar 2023.
An sameshi da aikata fashi da makami a ranar 22 ga watan Maris ɗin shekarar 2022, da su ka yi a Ado Ekiti, wamda su ka kwace babur da wayor hannu wanda ya saɓa da sashe na 314 da sashe na 312 (2) (a) na kundin manyan laifuka naa jihar.

Bayan ƴan sanda sun kamashi su ka gurfanar da shi a gaban kotu tare da hujjojin da su ka samu.

Alƙalin kotun Justice Olatawura Olalekan ya yankewa wanda aka samu da laifin hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Yayin da tuhuma ta farko aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai.
