Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce akwai ƙwarewa a salon yadda shugaba Tinubu ke jan ragamar mulkin Najeriya.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da ya tarbi shugaban hukumar hana fasa-ƙwauri ta ƙasa Kwastam a gidansa da ke Daura a ƙarshen makon jiya.
Buhari ya ce ya gamsu matuƙa da salon yadda shugaba Tinubu ke jagorantar mulkin Najeriya.

Ya ce yadda shugaba Tinubu ke mulkin ƙasar ba kowa ne zai jajirce a kan haka ba.

Shugaban hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya Kwastam Bashir Adewale ya yabawa shugaban bisa yadda ya ƙarfafafi sabbin dokokin aikin hukumar ma shekarar 2023.
Daga bisani shugaban ya kai ziyara fadar sarkin Daura wanda ya bayyanawa sarkin ceear, shugaba Tinubu ya basu umarnin mayar da dukkaanin kayan abincin da aka kama zuwa ga masu su don sauƙaƙa wahala da tsadar abinci da ake fuskanta a Najeriya.
