Majalisar dattawa ta kasa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya bisa zargin da ya yi na anyi kari a kasafin kudi na shekarar 2024.

Majalisar ta dakatar da Ningi ne na tsawon watanni uku bayan tafka wata doguwar mahawara da aka yi a zauren majalisar a zaman da aka gudanar a yau Talata.

A yayin zaman wani memba a kwamitin kasafin kudi na majalisar Jimoh Ibrahim shine ya fara gabatar da kudirin dakatar da Ningi na tsawon watanni 12 bisa zargin bada bayanan marasa kanshin gaskiya tare da kawo hatsaniya a cikin majalisar.

Bayan gabatar da kudurin da Ibrahim Jimoh ya yi wasu daga cikin ‘yan majalisar sun nemi da aka yiwa kudurin nashi gyaran fuska.

Inda wasu daga cikin ‘yan majalisar suka nemi da a rage adadin watannin zuwa watanni uku.

Sai dai bayan kammala gabatar da kudurorun da ‘yan majaisar su ka yi shugaban Majalisa Sanata Akpabio ya gudanar da wata kuri’a,wanda mafi yawan ƴan majalisar suka zaɓi amincewa da dakatar da Ningi na tsawon watanni uku.

Bayan kammala kada kuri’ar hakan ne ya sanya aka dakatar da Ninga bisa laifin da ya aikata na cewa shugaban Majalisar Sanata Akpabio ya yi cushe a karin kasafin kudin shekarar 2024 da muke ciki wanda shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.

Har ila yau sai dai bayan dakatar da Ningi ya sanar da yin murabus daga kan mukaminsa na shugaban kungiyar Sanatocin Arewa.

Sanatan Ningi ya ce ya yanke shawarar sauka daga kan mukaminsa ne bisa yadda abubuwan ke faruwa a majalisar a yankin Arewa da kuma Najeriya baki daya.

Daga karshe Ningi ya mika sakon godiya ga Sanatocin Arewa bisa jagorantarsu da yayi a matsayin shugaban kungiyar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: