Rahotanni na nuni da cewa akalla wasu fasinjoji 15 ne suka bace a yayin da ake zargin wasu ‘yan bindiga sun kaiwa motarsu hari a lokacin da suke tsaka da tafiya a Jihar Taraba.

Rahotanni sun bayyana cewa motar na dauke ne da mutane 18 wanda suka hada da mata da kananan yara a ciki.


Jaridar Leardership ta rawaito cewa motar da ke dauke da mutanen ta taso ne daga Zaki-Biam a Jihar Benue zuwa Maihura da ke cikin karamar hukumar Bali ta Jihar ta Taraba a ranar Talata.
Direban motar da ya tsere dauke da raunika ya bayyana cewa maharan na sanya ne da kayan jami’an sa-kai, dauke kuma da makamai a tare da su.
Shugaban karamar hukumar Ezra ya Tabbatar da faruwar lamarin.
Shugaban ya ce ya zuwa yanzu su na ci gaba da neman mutanen da suka bace a cikin dajin domin kubutar da su.
