Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin bai’wa masu kananan sana’o’i da kananan ‘yan kasuwa tallafin naira 50,000 domin bunkasa harkokin kasuwanci da kuma rage radadin halin da ake ciki a Kasar.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da bankin kasuwanci na Kasar ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa wadanda za su ci moriyar tallafin sun hada da masu sana’ar sayar da abinci, sufuri, ‘yan kasuwa, masu kananan sana’o’i da dai sauransu.

Kazalika sanarwar ta kara da cewa za ta bayar da tallafin ne ga wadanda suka cancanta ba tare da tilasta biyan kudin ba.

Sanarwar ta ce shirin zai bai’wa mata da matasa kaso 70 yayin da kuma za a bai’wa masu bukata ta musamman kaso 10.
Bugu da kari Kashi 20 din da ya yi ragowa za a bai’wa tsofaffi kashi biyar, sai kashi 15 kuma za a raba ga sauran mutane.
Ana sa ran mutane miliyan daya ne za su ci gajiyar tallafin daga dukkan kananan hukumomi 774 na fadin kasar da kuma birnin tarayya Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa wadanda za su ci gajiyar za su ci ne ta hanyar amfani da shaidar katin dan kasa ta NIN da kuma BVN.
