Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ya aike da ƙudirin ba da lamunin karatu da ya ƙudiri aniya a gaban majalisar dokokin ƙasar.

 

Shugaban majalisar wakilai a Najeriya Tajuddrn Abbas ne ya bayyana haka yau a zaman majalisar da ya gudana a yau Alhamis.

 

A wasiƙar da shugaban kasar ya aikewa da majalisar, ya buƙaci majalisar ta yi duba a kan ƙudirin da ya tsara dangane da ba da lamunin karatu da kuma waau dokoki da ke ƙarƙashin tsarin.

 

Lamunin karatun dai zai bai wa ɗaliban manyan makarantun Najeriya dama ta yin karatu ko da ba su da kuɗi.

 

A shekarar da ta gabata, shugaba Tinubu ya sha alwashin fara tsarin a watan Janairun ahekarar da mu ke ciki.

 

A ranar Laraba hukumar kula da manyan makaramtu a Najeriya ta shaida cewar, an samu taaikon tabbatar da tsarin ne bayan da majakisar dokokin ƙasar ta gano waau kura-kurai.

 

Sai dai a labaran da mu ka kawo muku a baya, ƙungiyar malaman jama’a a Najeriya ASUU ta yi watsi da tsarin, wanda ta ce zai bar ɗaluban ne cikin bashi tsawon rayuwarsu.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: