Masu garkuwa da su ka sace ɗalibai a Kaduna sun buƙaci a basu dala $620432 kwatankwacin naira biliyan guda.

Sannan sun yi barazanar kashe ɗaliban muddin ba a basu kuɗin ba nan da kwanaki 20.


Masu garkuwan sun tuntuɓi iyayen ɗaluban ne bayan da shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewar ba za a biya ko sisi ba domin sako su a jiya.
A ranar 7 ga watan Marisharamar ɗin da mu ke ciki ne ƴan bindigan su ka kai hari makarantar firamare ta Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun a Kaduna inda su ka sace ɗalibai har da wasu daga cikin malaman.
Wani mai suna Aminu Jubril da ke zama mai magana da yawun iyayen ɗaliban da aka sace, ya ce ƴan bindigan sun bukaci a basu naira biliyan guda domin sakin waɗanda aka sace.
Wani zabaɓɓen ahugaba a Kuriga Idris Ibrahim ya tabbatar da batun na ƴan bindigan.
Ya ce sun tuntuɓesu da ɓoyayyar lamba tare da buƙatar a basu kuɗin sannan sun ka sanya sharaɗin kwanaki 20 don ganin an biya kuɗin fansar ɗaluban.
A jiya, shugaba Bola Tinubu ya buƙaci a gaggauta kuɓutar da ɗaliban, tare da shan alwashin ƙin biyan ko sisi ka
[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]
fin sakinsu.
