Hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya Kwastam ta kama kayan sojoji a filin sauka da tashin jiragen sama na Legas.

 

Hukumar ta kama kayan sojin Najeriya tare da kwayoyin maye masu gudanr da tunani da bindigu.

 

An gano kayayyakin ne yayin da jami’an ke bincike a kan kayayyakin da aka shigo da su Najeriya.

 

Sai dai zuwa yanzu ba a bayyana ko an kama wasu da ake zargi ɗauke da kayan ba.

 

Wannan na zuwa ne watanni takwas bayan da hukumar ta kama wasu makamai a filin sauka da tashin jiragen sama na jihar Legas.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: