Ƙungiyar shuwagabannin jam’iyyar APC a Najeriya ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ya sauke duk wani shugaban hukumar tsaro da ya gaza a aikinsa.

Yayin da su ke yi wa manema labarai ƙarin bayani dangaje da ganawar da nsu ka yi da shugaban ƙasa a fadarsa yau Juma’a, shugaban ƙungiyar Alphonsus Oga Eba ya ce sun bai wa shugaban shawarar haka ne ganin yadda ake samun ƙaruwar hare-hare a Najeriya.


Ya ce barin irin haka na ci gaba zai shafi tauraruwar jamiyyarsu wanda hakan babbar tawaya ce a garesu.
Ƙungiyar ta yabawa shugaba Tinubu dangane da goyon bayan da yake bai wa jami’an tsaro a ko da yaushe, wanda su ka ce hakan ya sa su ka bashi shawarar sauke dukkan wanda ya gaza a aikinsa.
Ƙungiyar ta buƙaci shugaba Tinubu ya waiwaya tare da duba dukkan wani shugaban tsaro da ya gaza a aikinsa don saukeshi.
A cewarsu, hankalinsu ya tashi dangane da sace ɗalibai a Kaduna da sauran ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga da ke ƙara ta’azzara a ƴan kwanakin nan.
