Wasu mazauna garin Guringawa da ke karamar hukumar Kumbotso sun rasa matsuguni yayin da motar rusau ta gwamnatin Kano ta dira kan gidajensu.

A ranar Lahadi ne hukumar tsare-tsare da raya birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta rusa gidaje da dama a garin na Guringawa.
Wannan rusau dai na zuwa ne duk da umarnin babbar kotun jihar Kano, wadda ta dakatar da KNUPDA daga rusa gine-ginen al’umma a yankin.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadin, lauyan da ke kare masu kara 23 da aka rushewa gidajen, Abubakar Alhaji Rabi’u Doka, ya ce wadanda yake karewa sun samu umarni daga babbar kotun jihar.

Sai dai a cewarsa duk da wannan umarni na kotu, gwamnati karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi fatali da shi, ta aikata abin da ta yi niyya.
Lauyan ya ƙara da cewa waɗanda yake wa aiki sun mallaki filaye kusan 32 da rusau ya shafa kuma suna neman diyya bisa hanyar doka.
Manajan darakta na KNUPDA, Ibrahim Yakubu Adamu, bai amsa kira ko sakon saƙo da aka tura masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.