Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ciyar da mutane miliyan hudu a watan Ramadan na wannan shekarar a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Baba Dantiye ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kano, jiya Litinin.

Ɗantiyr ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan shida domin ciyar da marasa galihu a jihar da ke shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya.

Kwamishinan ya ce birnin Kano mai tarin jama’a wanda ya kunshi kananan hukumomi takwas ya na da cibiyoyi na musamman guda 90 na ciyarwa a watan azumi.

A cewarsa, cibiyoyin cikin birni da gwamnati ta ware domin ciyar da talakawa da gajiyayyu sun haɗa da masallatai, kurkuku, tsangaya, asibitoci da makarantun islamiyya.

Ya ce ana sa ran za a rabawa mutane 18,000 abinci kowacce rana har ƙarshen watan azumin Ramadan.

Ya ce kudin da aka ware ya haɗa da kuɗin kayan abinci, hayar kayan girki, alawus-alawus na dafa abinci da tsaro, itacen wuta da dai sauran duka a tsawon watan.

Tun da farko dai gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai kula da shirin ciyarwa a Ramadan wanda mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam ya kaddamar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: