Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana yadda ya ke magana da Shugaba Tinubu kan matsalar tsaron jihar.

Uba Sani ya ce a kullum ya na magana da Tinubu akalla sau biyu domin ganin an shawo kan matsalar tsaron a jihar.


Gwamnan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a birnin Abuja.
Ya bayyana cewa shugaba Tinubu da hafsoshin tsaro sun himmatu wurin tabbatar da kawo karshen matsalar tsaro a kasar.
Ya ce ya yi amanna da irin himmatuwar Tinubu wurin dakile matsalar tsaro ganin yadda ya ke nuna damuwa.
Ana ci gaba da samun rahotannin garkuwa da mutane da kashe-kashe wanda ya ƙara ta’azzara a kwanakin nan.