Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda, ya ce gwamnatinsa ba za ta nemi sulhu da ƴan bindiga a jihar ba.

 

A cewarsa, yin sulhun yana buɗe kofar ɓaraka ne ga matsalar tsaro, domin ƴan bindiga za su ɗauka gwamnati ba ta da sauran kataɓus.

 

Radda wanda ya nuna goyon bayansa kan kaddamar da ƴan sandan jihohi ya ce akwai bukatar gwamnoni su zama masu jan ragamar tsaro a jihohinsu.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ofishinsa a ranar Laraba a lokacin da ya karbi baƙuncin wakilan kamfanin Media Trust.

 

Radda ya ce dokar hukumomin tsaro ba ta ba gwamnoni damar juya akalar jami’an tsaro ba, don haka dole a rika samun tasgaro a harkar.

 

Radda ya ce abubuwan da ke faruwa a jihar ya sa ya dauki matakai na kashin kansa tunda ba shi da iko a kan jami’an tsaron tarayya.

 

Gwamnan ya ce matakin farko da ya dauka shi ne daukar alkawarin yaki da ‘yan bindiga ba tare da zaman sulhu ba, yana mai cewa gwamnatinsa ba ta gaza ba wajen magance matsalar a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: