Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya buƙaci al’ummar musulmi da su ƙara kaimi wajen addu’o’i a lokacin azumin watan Ramadan.

Gwamnan ya buƙaci su sanya mambobin rundunar tsaron jihar ta KCWC cikin addu’a domin yaƙar ƴan bindiga a ƙananan hukumomin da ake fama da matsalarsu.


Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wajen rabon hatsi ga mutane 2,000 da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Katsina ta tsakiya a majalisar wakilai, Danlami Musa ya ɗauki nauyi a tsohon gidan gwamnatin jihar da ke Katsina.
Radda ya ce Allah ya na amsa addu’o’i, musamman a cikin watan Ramadan lokacin da al’ummar musulmi suka himmatu wajen neman samun shiriya.
Ya yi alƙawarin ci gaba da ayyukan alheri da gwamnatinsa ta fara don inganta rayuwar al’ummar jihar.
Gwamnan ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na bayar da tallafi ga marasa galihu da mabuƙata a jihar.
Ya ce zai kuma ci gaba da bayar da alawus-alawus na wata-wata ga malaman addini da sarakunan gargajiya da ƴaƴan jam’iyyar APC mai mulki a jihar.
A kwanakin baya dai gwamnan ya ƙaddamar da rabon kayan tallafi ga al’ummar jihar domin azumin watan Ramadan.