Majalisar dattawa ta gabatar da kudurin hukunta iyayen da suka yi watsi da ƴaƴansu tare da ƙin tura su makarantar boko.

Sanata Adebule Idiat Oluranti ne ya gabatar da kudurin wanda ke nuna muhimmancin daƙile yawaitar yara marasa zuwa makaranta.


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta kuma duba yiwuwar kafa kotunan tafi-da-gidanka da za su wajabta ilimin zamani a kan kowane yaro.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya nemi gwamnoni da suyi amfani da dabarar da ya yi wajen shawo kan matsalar a lokacin yana gwamnan jihar Akwa Ibom.
Dabarar ita ce, yanke hukuncin dauri na watanni shida a kan iyaye ko iyayen riƙo da suka tura yaransu gona, aike ko talla alhalin lokacin zuwan yara namakaranta ne.
Da ya ke goyon bayan kudirin, Sanata Ahmed Lawan ya ce akwai yara sama da miliyan 20 wadanda ba sa zuwa makaranta a Najeriya.