Akalla dalibai mata biyu na Jami’ar jihar Nasarawa ne su ka iyarasa rayukansu sakamakon wani turmutsutsi a babban ɗakin taron jami’ar da safiyar Juma’a.

 

Wani shaidan gani da ido ya ce daliban da suka rasu na daga cikin wadanda suka yi tururuwar zuwa wurin rabon tallafi domin su samu tallafin.

 

Kamar yadda manema labarai suka ruwaito, lamarin ya faru ne lokacin da ɗaliban suka je wurin da gwamnatin jihar ta shirya rabon tallafin shinkafa ga ɗaliban.

 

An ce daliban sun kutsa cikin ma’ajin da aka ajiye kayan abincin da za a raba da safiyar Juma’a, suka ci ƙarfin jami’an tsaron makarantar da aka jibge a wurin.

 

An ruwaito cewa ɗaliban sun yi nasarar kutsa kai cikin rumbun ajiyar da misalin karfe 5:00 na asubahin ranar Juma’a, suka daka wa kayan tallafin wawa.

 

Ɗaliban da aka ware a matsayin waɗanda za su ci gajiyar tallafin an ba su katin shaida I.D. domin da katin ne kaɗai za su samu damar shiga wurin rabon tallafin.

 

An kuma ruwaitk cewa tun da misalin karfe 5 na safe dalibai suka mamaye wurin, inda suka yi galaba a kan jami’an tsaro, sannan suka kutsa cikin rumbun ajiyar.

 

Hakan ne ya haifar da turmutsitsi wanda ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar.

 

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan abin da ya faru daga mahukunta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: