Gwamnatin jihar Katsina tare da haɗin guiwar rundunar sojin saman Najeriya sun sake samun nasarar ceto mutum 17 da aka yi garkuwa da su.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, an ceto rukunin mutanen ne daga dajin Jibia wanda ke kan titin Jibia zuwa Ɓaure a jihar Katsina.


Wad’anda aka ceto sun fito ne daga kauyen Karofi da ke karamar hukumar Jibia a jihar kuma sun hada da matan aure uku da ƙananan yara 14.
Bayanai sun nuna cewa matan da ƙananan yaran da ba su wuce shekara biyar zuwa 10 a duniya ba, sun shafe kwanaki 15 a hannun ƴan bindiga.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ne ya tarbi mutanen da aka kubutar a madadin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa.
Danmusa ya kuma sanar da cewa gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko ta ɗauki lamarin tsaro da matuƙar muhimmanci domin zaman lafiya ya samu wurin zama a tsakanin al’umma.
Ya kuma tabbatar da kudirin gwamnatin jihar mai ci na kawo ƙarshen ‘yan ta’adda, inda ya kara da cewa tsaro shi ne abu na farko, na biyu, da na uku da gwamnatin ta sa a gaba.