Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna sun samu nasarar dakile wani yunkurin ‘yan bindiga na yin garkuwa da mutane akan hanyar Buruku zuwa Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Mansur Hassan ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Mansur ya bayyana cewa jami’an sun samu nasarar ne a yayin wani sintiri da jami’an suke gudanarwa a ko da yaushe a Jihar.

Kakakin ya ce kafin kubutar da mutanen sai da suka yi musayar wuta, wanda hakan ya sanya maharan suka tsere tare da shigewa cikin daji dauke da raunuka.

Mansur ya kara da cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 1:00 na rana akan babbar hanyar.
Bayan samun faruwar lamarin Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Audi Ali ya jinjinawa jami’an bisa nasarar da suka samu na dakile yunkurin na bata garin.
Sannan ya bukaci Al’umma da su kara sanya idanu tare da sanar da jami’an tsaro dukkan wani motsi da ba su yadda dashi ba.