Babban Alkalin Kotun Jihar Edo mai shari’a D.I Okungbowa, ya kafa wani kwamiti mai dauke da mutane Bakwai da zai yi aikin binciko zarge-zargen da ake yiwa mataimakin gwamnan Jihar Philip Shu’abu.

Alkalin ya kafa kwamitin ne a Jiya Juma’a kamar yadda aka tabbatar cikin wata takarda da magatakardar kotun ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta ce tsohon Mai shari’a S.A Omunua mai ritaya ne zai jagoranci kwamitin binciken.

Sanarwar ta kara da cewa Alkalin kotun ya kafa kwamitin ne karkashin sashi na 188 (5) na kundin tsarin mulkin Kasa na 1999.

Sanarwar ta bayyana cewa kwamitin zai binciki duk wasu zarge-zargen da ke kunshe a cikin takardar shirin tsige Shu’aibu wanda majalisar Jihar ta aikewa da Kotun.
Sanarwar ta ce da zarar kwamitin ya kammala binciken Alkalin kotun zai yanke hukunci akan matsayar tsige Mataimakin gwamnan na Edo.