Tsohon Mataimakin shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da wani hari da ‘yan bindiga suka kai hari a cikin Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Atiku ya bayyana hakan ne ta cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a.
Atiku ya ce harin da ‘yan bindiga su ka kai Kasuwar Kauyen Madaka da ke cikin karamar hukumar ta Rafi ya zama abin Alla-wadai a Kasar.

Dan takarar ya ce a halin yanzu Najeriya ta zama filin Mutuwa a karkashin mulkin shugaban Kasa Bola Tinubu.

Atiku Abubakar ya yi kira da aka gaggauta yiwa kundin tsarin mulkin Kasa Kwaskwarima, wanda hakan zai bayar da damar samar da ‘yan sandan Jihohi a Kasar domin kawo karshen matsalar rashin tsaro.
Atiku ya kara da cewa samar da ‘yan sandan Jihohi a Kasar hakan ne zai sanya su samar da hanyoyin da su ka dace a yankunansu don kawo karshen matsalar rashin tsaro.
Daga karshe Atiku ya yi addu’ar samun rahma ga wadanda suka rasa rayukansu a Jihar.
‘Yan bindigan sun kai harin ne a ranar Alhamis, inda suka hallaka magajin garin da wasu mutane 20, tare kuma da yin garkuwa da mutane da dama a Kauyen.
