A wani labarin kuma gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya musanta bayun satar ɗalibai 287 daga makarantar firamare ta Kuriga a jihar.

Gwamnan y ace ɗalibai 137 yan bindiga su ka sace maimakon 287 da ake yaɗawa.

Malam Uba Sanin a wannan bayani ne yayin day a tarbi ɗaliban da aka aka sace bayan da ƴan bindiga su ka sakesu kamar yadda ya shaida.

Ya gana da ɗaliban sannan aka miƙasu ga iyayensu.

Gwamna Uba Sani ya ce bai kamata a mayar da hankali kan batun ko said a aka biya kuɗin fansa kafin sakinsu ba, ko kuma ba a biya ba.

Y ace abu mafi muhimmanci bai wuce yadda gwamnatin ta yi iya ƙoƙarinta don ganin ta kuɓutar da ɗaliban ba.

Gwamnan ya nuna rajin daɗinsa kan yadda ake tuhuma ko said a aka biya kuɗin fansa kafin sakin ɗaliban.

An sace ɗaliban ne a ranar 7 ga watan Maris ɗin  da mu ke ciki, a makarantarsu da ke Kuriga a jihar Kaduna sai dai an ganosu ne a wani daji da ke jihar Zamfara.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: