Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gayyaci fitaccen malamin nan Sheik Ahmad Mahmud Gumi domin amsa tambayoyi.

Gwamnatin ta gayyaci malamin ne bayan day a matsa da yin kalamai dangane day an bindiag wanda yak e nuna kuskuren gwamnatin kan matakan da ta ke ɗauka.
Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ne ya bayyana haka yau Litinin yayin ganawa da manema labarai a fadar shugaban ƙsa.

Ya ce Shek Gumi bai fi ƙarfin doka ba, domin haka ba wani abin makamaki ba ne don gwamnatin ta gayyaceshi domin amsa tambayoyi.

Sheik Gumi ya na caccakar gwamnatin a kan yadda ta ke tafiyar da al’amuran yaƙi da ƴan bindiga a ƙasar, wanda y ace kyautuwa ya yi a yi sulhu das u maimakon ci gaba da yaƙarsu.
Ko a kan batun satar ɗalibai na Kuriga a Kaduna, said a Gumi ya bayyana cewar bai kyautu gwamnatin ta bayyana aniyar karɓisu ta kowanne hali ba.