Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a titin Miller Road ta yankewa dan kasar Chinan nan da ya hallaka budurwar Ummukulsum Sani Buhari da aka fi sani da Ummita hukuncin kisa ta hanyar rataya.

 

Alkalin Kotun mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji ne ya yanke hukuncin a zaman da kotun da ya gudanar a yau Talata.

 

Ma’aji ya yanke hukuncin ne bayan gamsassun hujjojin da aka gabatarwa da Kotun a kan dan Kasar ta China da ya hallaka ummita.

 

Masu kara karkashin jagorancin Kwamishan shari’a na Jihar Haruna Isa Dederi, sun bayyanawa kotun cewa a ranar 16 ga watan Satumba na shekarar 2022 dan Kasar ta China ya yi amfani da wuka wajen hallaka Ummita a Gidansu da ke Unguwar Jambulo a jihar.

 

A yayin zaman shari’ar masu kara sun gabatarwa da kotun hujjoji guda hudu, yayin da kuma lauyan wanda ake karewa ya gabatarwa da kotun hujjoji Biyar.

 

Bayan kammala yanke hukuncin Lauyan wanda ake kara ya nemi da kotun ta yiwa dan kasar ta China rangwame game da hukuncin da kotun ta yanke masa.

 

Daga bisani Lauyan ya ce wanda ake karar zai daukaka kara zuwa kotun gaba

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: