Rundunar Sojin Najeriya ta gudanar da bikin sakin mutane 200 wanda rundunar ta wanke daga zargin aikata laifukan Boko-Haram a Kasar.

Taron sakin mutanen ya gudana ne a safiyar yau Talata a hedkwatar sojojin Giwa da ke garin Maiduguri a Jihar.


Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami’an sun kama mutanen ne a lokacin da ayyukan ‘yan ta’addan ke kara yawaita a Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan kammala bikin wanke mutanen za a mika su ne ga gwamnatin Jihar ta Borno, domin su ci gaba da rayuwa a cikin mutane.
A yayin mika mutanen kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na Jihar da kwamishinar mata da walwalar jama’a ne su ka karbi mutanen amadadin gwamnan Jihar Babagana Zulum.