Gwamnan JIhar Borno Babagana Umara Zulum ya amince da nada mutane 168 da za su yi aikin taimaka masa a bangarori daban-daban.

 

Zulum ya kuma sake nada mutane 104 a matsayin ‘yan majalisar gudanarwa na hukumomin da ma’aikatun gwamnati 15 a Jihar.

 

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Alhaji Tukur Tijjani ya fitar a ranar Litinin.

 

Bukar ya ce gwamna Zulum ya yi nadin ne bisa tanadin sashi na 208 (2) na kudin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999.

 

Sanarwar ta kara da cewa bayan nadin gwamnan ya taya wadanda ya nada murna, tare da yin kira a garesu da su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata domin kawowa Jihar ci gaba.

 

Nadin da Zulum yayi na zuwa ne kwanaki kadan bayan gwamnan ya bayar da umarnin fitar da naira biliyan 2.1 domin biyan ma’aikata da ‘yan Fansho a Jihar

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: