Bbbar kotun jihar Kano ta tabatar da dakatarwar da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Ganduje su ka yi wa tsohon gwamnan Kano Dakta Abdullahi umar Ganduje.

Ƙarar da Laminu Sani da Haladu Gwanjo su ka shigar gaban kotun, sun jaddada matsayarsu na dakatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin ɗan jam’iyyar daga mazaɓarsa ta Ganduje.

Tun a ranar Litinin aka wayi gari da labarin wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwar jam’iyyar a mazaɓar Ganduje, das u ka sanar da dakatar da tsohon gwamnan daga cikin jam’iyar.

Sai dai daga bisani shugaban majalisar a matakin mazaɓa da shugaban majalisar na ƙaramar hukumar Dawakin Topa da ma shugabancin majalsiar a matakin jiha sun yi watsi da batun.

Jam’iyyar ta zargi mutane biyun das u ka shigar da ƙarar da cin amanar jam’iyyar, ta hanyar yi wa jam’iyyar adawa aiki kamar yadda shugaban jam’iyyar na ƙaramar hukumar Dawakin Topa ya shaida.

A hukuncin da mai shari’a Usman Malam Na’abba ya yanke a ranar Talata, ya tabatar da matakin da mambobin biyu daga cikin tara su ka ɗauka na dakatar da Ganduje daga cikin jam’iyyar.

Bayan faruwar haka, jamiyyar APC ta zargi abokiyar hamayyarta ta NNPP da hannu a lamarin das u ka kira maƙarƙashiyar.

Sai dai tuni jam’iyyar NNPP ta nesanta kanta da hannu a ciki, wada ta ce lamari ne da ya shafi jam’iyyar APC kuma abu ne na cikin gida babu hannunsu a ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: