Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar gano wani sansanin mayaƙa Boko Haram da ISWAP a dajin sambisa tare da lalatashi sannan su ka ƙwato makamai.

A wata sanarwa da rundunar ta sanar a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya, rundunar ta ce sun tarwatsa sansanin mayaƙan sannan sun lalata wasu makamai tare da ƙato wasu.


An kai harin ne Ngumne, Kawaran, Mangu duka a dazukan Sambisa da Tinbuktu a jihar Borno.
Rundunar ta yi amfani da makamai masu hatsari wajen tarwatsa sansanin sannan an ƙato manyan bindigu da hasashi da wasu makamai.
Ta ce hakan na daga cikin ayyukan da ta ke yin a kawar da dukkanin ayyukan ta’addanci da ake aikatawa a jihar.
Jihar Borno na fama da rikicin mayaƙan ISWAP da Boko Haram fiye da shekaru 10 da su ka gabata.