Aƙalla mutane 45 ne su ka rasa rayuwarsu bayan ɓullar wata annoba a Kano.

 

Mutane a ƙauyen Gundutse a ƙaramar hukumar Kura a Kano na jimamin rasuwar mutane 45 mafi yawa daga ciki mata ne da ƙananan yara bayan da wata annba ta ɓarke a ƙauyen.

 

Al’amarin ya faru ne bayan da mafi yawa daga cikinsu su ka nuna alamar kamuwa da zazzaɓin cizon sauro, mashaƙo da ama.

 

Al’ummar sun shida ɗimuwa bayan da ake rasa mutane biyar a kowacce rana.

 

Wani mazaunin garin mai suna Abu Sani ya shaida cewar, ya rasa ƴaƴansa gida biyu wanda ya yi tunanin ko zazzaɓin cizon sauro ne ya yi ajalinsu.

 

Wata mai suna Hajara Abubakar ta ce zuwa yanzu ta san mutane 40 da su ka mutu a sakamakon annobar.

 

Yahaya Tijjani Kura da ke zama shugaban riƙo na ƙaramar hukumar, ya tabbatar da faruwar hakan sai dai y ace zuwa yanu mutane uku ne su ka mutu.

 

Yayin dama’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce bat a da masaniya dangane da faruwar lamarin zuwa yanzu, domin bas u samu sanarwa a hukumance daga ƙaramar hukumar ba, sai dai ana gudanar da bincike a kai.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: