Ƙungiyar masu buƙata ta musamman ta arewacin Najeriya ta koka a kan yadda ake sake mayar da su baya duk da cewar an zaɓo ɗan cikinsu tare da bashi muƙami a fadar shugaban ƙasa.

Yarima Sulaiman Ibrahim shugaban ƙungiyar na arewa, shi ne ya bayyana haka yayin ganawa da Matashiya TV yau Laraba.


Abba Isah shi ne mashawacin shugaban ƙasa a kan masu buƙata ta musamman wanda aka zaɓo daga jihar Yobe.
Ya ce dun da an zaɓo ɗan cikinsu kuma aka masa mashawarcin shugaban ƙsa kan masu buƙata ta musamman, bay a yin abinda ya kamata.
Y ace maimakon ya mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ga masu buƙata ta musamman, sai ya fi karkata wajen raba abinda bai kai ya kawo ba.
A sakamakon haka y ace ba za su lamunta ba domin a wannan lokaci ana samun ƙaruwar mabarata daga cikinsu maimakon raguwarsu.
A don haka su ka yi koka domin a cewarsu, ba ya yin abinda ya kamata wajen sauke nauyin da ke wuyansa.
Za ku samu cikakkiyar tattaunawar a shafukanmu na YouTube da Facebook.