Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana dalilan da ya sanya ake ci gaba da samun yawaita matsalar tsaro a Kasar.

Mai bai’wa shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu shi ne ya bayyana dalilan da ke kara haifar da yawaitar matsalar rashin tsaro a fadin Najeriya.
Ribadu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Jihar Sokoto.

A yayin jawabin na Malam Nuhu ya ce yawaitar shigo da kananan makamai, da cin hanci da rashawa da kuma rashin adalci ne suke kara haddasa rashin tsaro a Kasar.

Ribadu ya kara da cewa duk da dokar hana mallakar makamai a kasar ba tare da izinin hukuma ba, a halin yanzu wasu mutanen na ta yawo da kananan makamai wanda hakan shima na kara haddasa tashin hankula a Kasar.
Kazalika Malam Ribado ya ce gwamnatin shugaban Bola Tinubu ta dauki matakai da dama na rage yawaitar kananan makamai wanda kuma hakan ya samar da kyakykyawan sakamako mai kyau a Kasar.
Ya kara da cewa a karkashin jagorancin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu an samu ingantaccen tsaro sosai a yankin Neja Delta wanda hakan ya taimaka wajen habaka harkokin mai a yankin.