Hoton man feturMan Fetu

Matatar mai ta Dangote ta nesanta kanta da samar da man dizal wanda ba ingantacce ba a Kasar.

Mai magana da yawun matatar Anthony Chiejina shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Juma’a.

Matatar ta yi watsi da jita-jitar da ake yadawa akan hakan, inda ta ce babu kamshin gaskiya a rahotannin da ake yadawa.

Sanarwar ta ce an fitar da labarin domin bata sunan matatar, inda kuma ta ce ta na samar da ingantaccen man dizal wanda ya ke da karko dai-dai da kasuwannin duniya.

Kazalika ya ce su na samar da man na Dizal mai kyau fiye da wanda ake shigowa da shi Najeriya.

Antony ya ce kwata-kwata labarin bashi da tushe balle makama dn haka muutane su yi watsi da batun.

Sannan ya kara da cewa rage farashin da kamfanin ya yi baya rasa nasaba da cikar da ake yi a kamfanin domin neman dizal din da kuma yanayin sauye-sauyen kasuwa da aka samu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: