Dangane da sabuwar sanarwar dakatar da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, jam’iyyar APC a Kano ta magantu, wanda ta ce waɗanda su ka yi hakan ba ƴan jam’iyyar ba ne.

A safiyar yau Lahadi ne wasu da su ke iƙirarin shugabannin jam’iyyar ne a mazabar Ganduje su ka yi taron manema labarai tare da sanar da cewar sun dakatar da Ganduje daga cikin jam’iyyar.

Abdullahi Ganduje dai shi ne shugaban jam’iyyar APC a ƙasar.

Bayan fitar da sanarwar ne sakataren jam’iyyar a Kano Ibrahim Zakari Sarina ya shaidawa wakilin jaridar Daily Trust cewar waɗanda su ka fitar da sanarwar ba ƴan jam’iyyar ba ne.

Ko a farkon makon da mu ke ciki sai da aka samu wannan dambarwa, wanda wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar APC a mazabar Ganduje su ka bayyana dakatar daa shugaban jam’iyyar.

Har ma su ka je babbar kotun jihar Kano ta tabbatar da dakatarwar.

Sai dai daga bisani Ganduje ya garzaya kotun tarayya wadda ta jingine wancen hukunci na kotun jiha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: