Dakarun soji na Operation Lake Sanity da na Operation Haɗin Kai sun gano wani gidan biredi mallakin ISWAP a jihar Borno.

Masanin tsaro kuma mai sharhi kan al’amuran tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ya bayyana a shafinsa.
Ya ce jami’an sun yi aikin haɗin gwiwa tare da gano gidan biredin mallakin mayakan a jiya Lahadi.

Tuni su ka lalata gidan biredin tare da kwato wasu kayyaki.

A makon da ya gabata ne dai jami’an su ka lalata wasu sansanin mayakan da su ka addabin wasu yankuna a jihohin Borno da Yobe da hare-hare.
Ko a jiya sai da mu ka kawo muku labari cewar mayaƙan na shirin buɗe gidan rediyo domin watsa shirye-shirye a arewa maso gabashin ƙasar.