Wasu ‘yan bindiga da su ka addabi garuruwan karamar hukumar Wase a jihar Filato sun ajiye makamansu tare da miƙa wuya.

Gwamnatin jihar Filato ta sanar da hakan a ranar Litinin inda ta ce ‘yan bindigar masu yawa sun mika bindigogi kirar AK47 ga gwamnatin jihar.


Mai ba Gwamna Caleb Mutfwang shawara kan harkokin tsaro, kuma kwamandan rundunar Operation Rainbow, Birgediya Janar Gakji Shippi ya bayyana hakan a Jos.
Shippi ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun mika wuya tare da ajiye makaman nasu ne bayan doguwar tattaunawa tsakanin su da gwamnati.
Ya ce baya ga bindiga kirar AK47, akwai kuma sauran makamai da ‘yan bindigar suka ajiye wanda ya nuna sadaukarwarsu ga zaman lafiya.
Mai ba gwamna shawarar ya yi kira ga sauran ‘yan bindiga a jihar da su mika wuya tare da ajiye makamansu.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar ta dauki matakai na ƙwato makamai daga kungiyoyin ‘yan ta’adda domin daƙile hare-hare a karamar hukumar Wase.