An samu tashin gobara a filin sauka da tashin jiragen sama na ƙasa da ƙasa Murtala Muhammad da ke birnin Legas.

 

A sakamakon tashin wutar, hukumomin tashar sun sauya gurbin tashin jiragen sama don kaucewar wutar da ta barke.

 

Barkewar wutar ta faru ne a sanyin safiyar yau kamar yadda aka shaida

 

Mai maagana da hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta ƙasa Misis Obiageli Orah ta tabbatara da tashin wutar, sai dai ta ce an samu dauki daga kwararrun masu kashe wutar na tashar wanda su ka kai ɗaukin gaggawa.

 

Ta ce ana zargin tashin wutar na da alaka da wutar lantarki, sai dai har zuwa yanzu ana ci gaba da bincike a kai.

 

Tuni aka dakatar da ayyukan tashi da saukar jirage a wajen da lamarin ya faru, yayin da su ka sauya wani wajen daban duka a cikin tashar jirgin saman.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: