A sakamakon tsananin zafi da ake fuskanta, manoma kaji na tafka asara wanda hakan ya jefa da manoma da dama cikin mawuyacin hali.

 

Shugaban kungiyar manoma kaji ta jihar Kano Dakta Usman Gwarzo ya shaidawa Matashiya Tv cewar, tsananin zafin da ake fuskanta na yin silar kutuwaar kajin wanda manoman ke cikin fargaba.

 

Ya ce a kowacce shekara manoma na shiga damuwa a watanni Maris, Afrilu, Mayu da Yuni saboda tsananin zafin da ake fuskanta.

 

Sai dai ya koka a kan yadda da yawa daga cikin manoma kajin ba sa shiga cikin ƙungiyar wanda hakan ke taimakawa wajen yawan mutuwar kajin saboda rashin samun kwarewa da yadda za su tafiyar da kajin a irin wannan lokaci.

 

Ya ce zuwa yanzu babu wata ƙididdiga da za ta nuna yawan kajin da ke mutuwa a kowacce rana, ko kuma zuwa wannan lokaci a bana domin ba kowa ke basu rahoto a kan yadda kajinsu ke mutuwa a kullum ba.

 

Dangane da batun tallafi da gwamnatin tarayya ta ce za ta basu kuwa, Dakta Usman Gwarzo ya ce har kawo wannan lokaci, babu wani abu da gwamnatin ta yi, yayin da tuni su ka mika adadin manoman da ke karkashinsu da kajin da su ke da shi

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: