Mazauna gidan gyaran hali sama da 100 su ka tsere bayan da wata katanga ta rushe a jihar Neja.

Hukumar gidajen ajiya da gyaran halin a jihar sun tabbatar da haka, wanda su kaa ce mazauna gidan sun gudu ne sakamakon faduwar wata katanga a gidan.


Faduwar katangar ta faru ne sanadin ruwan sama da iska mai karfi da aka samu a jiya Laraba.
A wata sanarwa da su ka fitar yau Alhamis, mai magana da yawun hukumar a Abuja Adamu Duza ya ge an gano mutanen da su ka gudu sun kai su 118.
Sanarwar ta tabbatar da faduwar katangar sanadin ruwan sama mai karfi, wanda hakan ya baiwa mazauna gidan damar guduwa.
Sai dai an samu nasarar kama guda goma daga cikin wadanda su ka gudu bayan da su ka hada kai da sauran jami’an tsaro.
Sannan hukumar ta bukaci Mutane da su koma bakin harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.