Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu da dama a jihar Zamfara.

Harin da su ka kai a jiya da daddare, sun lalata karfen sadarwa na kayin waya wanda hakan ya hana damar sadarwar a garin.


Yaan bindigan sun kai hari garin Dauran a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar
Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar hakan yau Alhamis.
Ya ce mutane uku aka kashe a garin yayin da aka yi garkuwa da wani mutum guda.
Sannan sun kone wata tashar sadarwar layin kira na MTN a garin.
Ƴan bindigan sun shiga garin dauke da muggan makamai.
Mazauna garin sun shaida cewar an kashe mutane uku sannan an yi garkuwa da wasu mutane da ba a kai ga ganosu yawansu ba a masarautar Zurmi.
A garin na Dauran kuwa, an yi garkuwa da mutane biyar