Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta bayyana cewa an ceto mutane da wani gini mai hawa uku da ake ginawa a unguuwar Kuntau ya fado musu a Jihar.

Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar faruwar Lamarin a yau Juma’a.

Saminu ya ce Lamarin ya faru ne da safiyar yau Juma’a a lokacin da ake tsaka da gudanar daginin.

Kakakin ya ce mutane uku sun rasa rayukansu a yayin da aka ceto biyar da ransuu.

Saminu ya kara da cewa wadnda suka jikkata an kaisu zuwa Asibiti domin basuu kulawar gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: