Gwamnatin Jihar Legas ta musanta rade-radin da ake yadawa gwamnatin Jihar ta amince da mafi makarncin albashi na naira 70,000 ga ma’aikatan Jihar.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Gbenga Omotosho shi ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Juma’a.

Kwamishinan ya ce mutane na yada cewa gwamnatin Jihar za ta daina biyan ma’aikatan Jihar naira 35,000 inda za ta koma biyansu naira 70,000.

Kwamishinan ya kara da cewa ana yada irin wadannan zantukan ne bayan gwamnan Jihar ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin Tarayya za ta fitar da sabon mafi karancin albashi a kasar.

Omotosho ya ja kunnen masu yada irin wadannan labaran marasa kanshin gaskiya da su gujewa aikata hakan.

Sannan Omotosho ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a jita-jitar da ake yadawa don haka ya bukaci mutane su yi watsi da ita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: