Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Imo Gerald Irona ya yi murabus daga jam’iyyar PDP tare da wasu mutane hudu.

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa, Gerald Irona ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyyar ne a cikin wata wasika da ya aikewa da shugaban Jami’iyyar na mazabar Oguta da ke karamar hukumar ta Oguta a jihar.
Irona ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar ne bisa yadda jam’iyyar ta ke gudanar da al’amuranta tare da sauya tsarin jami’iyyar kamar yadda wadanda suka kafata suka dora ta a kai.

Irona ya kara da cewa ba zai gamsu da irin yadda jam’iyyar ta ke gudanar da harkokin ta ba.

Mutane biyar din da suka fice daga jam’iyyar su ne baya-bayan daga cikin mambobin jam’iyyar da suka fice daga cikinta a Jihar ta Imo.