Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun hallakka wani kwamandan rundunar sojin Najeriya da ke sansanin sabon garin Dan Ali da ke karamar hukumar Dan Musa ta Jihar Katsina.

Maharan sun hallaka Kwamandan ne a yayin wani harin kwanton bauna da suka kai garin da yammacin jiya Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an kaiwa kwamandan hari ne a kauyen Malali da ke Karamar hukumar Kankara ta Jihar.

Wasu majiyoyi daga garin sun bayyana cewa maharan sun hallaka Kwamandan ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kai dauki domin dakile harin ‘yan bindigar a kauyen, bayan mazauna garin sun nemi dauki daga gareshi.

Majiyoyin sun ce kauyen na Malali ‘yan bindigan sun kwace shi inda suka addaba musu da kai hare-hare.

Majiyoyin suun kara da cewa kafin dauko gawar kwamandan da jami’an sojin suka yi sai da suka yi musayar wuta da maharan.

Sai dai bayan hallaka Kwamandan an dauke gawarsa tare da kai ta wani Asibiti da ke Jihar ta Katsina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: