Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada shugaban hukumar kula da Muhalli ta Kasa NESREA, da kuma shugaban hukumar raya kogin Neja-Delta NDRBDA na Kasa.

Mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Ajuri ya ce shugaban ya nada Dr Innocent Bariate a matsayin shugaba a Hukumar Kula da Muhalli ta Kasa, ya yin da shi kuma Prince Ebitimi Amgbare za ta rike shugabancin hukumar raya kogin Neja Delta.

Kafin nadin mutanen sun rike mukamai daban-daban a Jihohinsu.

Dr Barikor ya kasance tsohon mamban a majalisar dokokin Jihar Rivers daga shekarar 2011 zuwa 2015, ya yin da Prince Amgbare a baya ya rike mukamin jami’in rundunar sojan ruwa sannan kuma tsohon kwamishina ne a Jihar Bayelsa.
A yayin nade-naden shugaban ya bukacesu da su yi aiki tukuru tare da rikon amana ga al’ummar kasa.