Hukumar kula da tashoshin jiragen sama a Najeriya FAAN ta rufe wani titi da ke filin sauka da tashin jiragen sama na Legas bayan da wani jirgi ya zame daga titinsa.

Hakan na zuwa ne kwanaki 16 bayan da jirgi mallakin kamfanin Dana ya zame wada hakan ya sa aka jinkirta tashi da saukar jiragen sama.

Lamarin ya sake faruwa a yau wanda jirgi mallakin kamfanin XEJET ya zame daga titinsa.

Jiin na dauke da mutane 52 wanda ya taso daga birnin tarayya Abuja.

A sakamakon haka hukumar FAAN ta rufe titin mai lamba 18/left na filin jirgin.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: