Fiye da mutane 200 ne su ka rasa rayuwarsu bayan da wata ambaliyar ruwan sama ta faru a ƙasar Afghanistan.

Majlaisar ɗinkin duniya ce ta sanar da haka wanda aka saka dokar ta ɓaci tare da ƙoƙarin ceto mutanen da su ka jikkata.

A jiya Juma’a aka samu wani ruwa mai ƙarfin gaske wanda ya haifar da ambaliyar a arewacin Baghlan yankin da ake noma a ƙasar.

Dubban gidaje ne su ka rushe yayin d amutane sama da 200 su ka mutu sanadin ambaliyar ruwan.

Wani taga cikin gwamnatin Taliban ya ce mutane 62 sun mutu a jiya Juma’a da daddare.

Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ma ya wallafa lamarin a shafinsa na X yau Asabar.

Tuni aka saka dokar ta baci domin samun damar ceto rayukan mutanen a su ka jikkata.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: