Wasu hadɗura biyu da su faru a jihar Ogun yayi silar raunata mutane 17 yayin da sama da 15 su ka tsallake rijiya da baya.

Lamarin ya faru a yau a misalin ƙarfe 08:55am na safe a kusa da gadar Iju da ke kan hanyar Ota-Idiroko wanda mutane 17 su ka jikkata wasu 15 tsira.

Hatsarin biyu da su ka faru ya shafi motoci uku da babur mai kafa uku wanda aka fi sani da adaidaita sahu.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura a jihar Florecent Okpe ta tabbatar da faruwar haka a yau.

Ta ce lamarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da direbobin motar ke yi wanda haka yas su ka kasa sarrafa motarsu.

Ta ce waɗanda su ka jikkata an kaisu baban ainitin Ota domin samun kulawa daga likitoci.

Sannan hatsarin ya shafi mutane 32 wanda ya haɗa da maza 12 mata 20.

Waɗanda su ka jikkata akwai maza shida mata 11 yayin da mutane 15 su ka tsira.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: