A jihar Filato kungiyar kwadago ta rufe ofishin rarraba hasken wutar lantarki a Jos babban birnin jihar yayin da su ka gudanar da zanga-zangar lumana a yau.



Mambobin kungiyoyin sun cika a kofar shiga hukumar kula da lantarki ta ƙasa.
Yayin zanga-zangar an hango jami’an tsaron DSS, ƴan sanda, da hukumar kare faararen hula ta NSCDC.
Matakin rufe ofishin rarraba hasken lantakin ya biyo bayan ƙara farashin wutar da aka yi a kwanakin nan wanda ƙungiyar ta ce ba za ta lamunta ba.
Ƙungiyar ta buƙaci a soke batun ƙarin wutar wanda ta ce ba za ta lamunci haka ba.
Kungiyoyin sun ɗauki maatakin zanga-zangar ne wanda su ka karade ofisoshin rarraba wutar na jihohin Najeriya.